Abdul Tech Systems Ltd
Labarai

An Kama Matashi Da Kullin Tabar Wiwi 39 A Kano

Published by Zainab Sabitu

An gurfanar da wani matashi dan shekaru 25 a gaban kotun shari’ar Musulunci da ke Fagge a Kano bisa zarginsa da mallakar wasu kulli 39 da ake zargin na Tabar Wiwi ne.

Matashin, mai suna Ibrahim Shehu, wanda mazaunin unguwar Kwana Hudu ne a birnin Kano, na fuskantar tuhumar mallakar Tabar ta Wiwi.

Ko da yake wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, amma alkalin kotun, Mai Shari’a Bello Khalid, ya ba da umarnin a garkame shi a gidan gyaran hali.

Tun da farko dai, dan sanda mai shigar da kara, Abdul Wada, ya shaida wa kotun cewa an cafke Ibrahim ne ranar 22 ga watan Fabrairun 2022 yayin wani sintiri.

Ya ce an kama shi ne wajen misalin karfe 8:00 na dare da kulli 39 na tabar, laifin da ya ce ya saba da sashe na 137 na Kundin Dokar Shari’ar Musulunci na Jihar Kano.

Daga nan alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 14 ga watan Maris domin yanke hukunci.

🤞 Don’t miss any Article!

We don’t spam! Read more in our Privacy Policy.

Oh hi there 👋
Don't miss anything.

Sign up to receive awesome content in your inbox.

We don’t spam! Read our Privacy Policy for more info.

About the author

Zainab Sabitu

I'm who I am and that's just enough.
I'm definitely the best of my kind.
Just take a seat and grab a cookie.

Leave a Comment