LabaraiWorld News

Askarawan Saudi Sun Kama Mabarata Kusa Da Ka’aba

Jami’an tsaro a kasar Saudiyya da ke birnin Makkah sun kama wasu mazauna birnin bisa zargin su da yin bara, yayun da aka cafke wasu mutum biyu a kusa da masallacin Ka’aba.

Hukumomin sun ce sun kama wani dan kasar Indiya bisa kokarin karkatar da hankulan masu ibada domi su ba shi kudi, sannan sun damke wani dan asalin kasar Moroko da yake bara a jikin wata kofar shiga masallacin na Ka’aba kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Mabarata a Saudiyya

Akwai kuma wani dan kasar Yemen wanda ke amfani da sandunan guragu domin yaudarar masu ibada cewa shi mai fama da nakasa ne.

Kana an kama wani mutum da ke tura dansa ya yi bara ta hanyar saka shi a kan keken guragu, I da bincike ya tabbatar da cewa dan nasa kalau yake.

Hukumar da ke kula da tsaron al’umma ta Saudiyya ta sanar cewa duk wanda aka kama yana bara, ko kuma wanda ya iza wani ya yi bara, ko ma ya amince da yin barar – zai shafe kusan shekara guda yana zaman gidan kaso ko ya biya tarar Riyal 100,000 ko ma duka.

Leave a Reply