Education

Gwamna El-Rufai Na Jihar Kaduna Zai Kori Malamai 233 Daga Aiki Saboda Takardun Bogi

Gwamnatin Jihar Kaduna za ta kori malaman makaranta 233 bisa laifin amfani da takardun shaidar karatu na bogi.

Shugaban Hukumar Kula da Ilimi a Matakin Farko na Jihar Kaduna (KADSUBEB), Tijjahi Abdullahi, ya ce nan gaba kadan hukumar za ta gudanar da jarrabawa ga malaman makarantun firamare da sakandare a jihar.

Tijjani ya ce ya zama dole a kori malaman da ke amfani da takardun bogi domin hana su lalata ingancin bangaren ilimi a jihar.

A cewar sa, a baya bayan nan, malamai 233 daga cikin 451 da aka tantance suna amfani ne da takardun bogi, inda ya kara da cewa akwai cibiya daya da ta nesanta kanta da malamai 212 da daga cikin takardun bogi 233.

Yace hukumar za ta kori malamai 233 da ke amfani da takardun bogi, sannan ta tura wa Ma’aikatar Shari’a takardunsu domin ta gurfanar da su a gaban kuliya manta sabo, domin tabbatar da adalci, Jibrin yace za’a wallafa sunayen malaman da aka gano suna amfani da takardun bogi a shafin Gwamnatin Jihar Kaduna.

Shugaban hukumar KADSUBEB ya ce bayyana sunayen zai kara daga darajar jihar, da kuma bunkasa fanni ilimi a jihar.

A cewarsa hakki ne a kan hukumar ta tabbatar da cewa malaman da ke koyarwa a makarantun gwamnatin jihar sun cancanta kuma suna da sahihan takardun .

A kan haka ne, a watan Afrilu ta kafa kwamitin tantance takardun da malaman suka gabatar domin tabbatar da suna da duk abin da ya dace a dauke su aiki a makarantun firamare da sakandare.

Ya ce hukumar ta tantance takardun malamai 451 ta hanyar tuntubar cibiyoyin da suke ce sun ba su takardun, 9 daga cikinsu kuma suka amsa kira.

Sai ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da aikin tantance takardun malamai domin tabbatar da sahihancinsu.

Idan za’a iya tunawa dai, a shekarar 2017 ne gwamnatin jihar ta dauki sabbin malamai 25,000, inda ta bayyana cewa za ta rika tantance su domin tabbatar da yadda suke samun ci gaba a aikinsu da kuma koyar da dalibai.

Leave a Reply