Rabiu Kwankwaso, ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, ya ce ba zai bari a lalata harkokin tashoshin ruwa yadda aka saba ba idan aka zabe shi a 2023.
Ya ce Najeriya na bukatar ingantaccen tsari a ɓangaren teku domin ta kasance mai matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin kasar.
Mista Kwankwaso ya kuma yi kira da a gaggauta gyara tare da rage cunkoso a hanyar shiga tashar ruwa ta Apapa a jihar Legas.
Ɗan takarar shugaban ƙasa r na jam’iyyar NNPP ya yi wannan kiran ne a wani taro da masu ruwa da tsaki a harkar ruwa da kamfanin Prime Maritime Project ya shirya a Legas a yau Talata.
A cewar Kwankwaso, lallai kasar nan na bukatar ta tsara yadda za a samu ci gaba a fannin teku domin yana da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa da kuma ci gaban tattalin arzikin kasar.
Leave a Comment