Labarai

Kotu ta yi watsi da buƙatar PDP da LP ta nuna zaman kotu a talabijin

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta Najeriya ta ki amincewa da bukatar yada zaman shari’ar ta kafafen yada labarai kai tsaye, kamar yadda masu korafi manyan ‘yan hamayya suka bukata.

Dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata na 2023 Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP suka bukaci a rika yada shari’ar kai tsaye, kamar yadda shi ma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour tare da jam’iyyar tasa Peter Obi suka gabatar da wannan bukata ga kotun.

A sanarwar hukuncin da kotun ta yi wadda bakin alkalanta biyar ya zo daya ta ce bukatar ba ta da cancanta inda jagoran masu shari’ar Justice Haruna Tsammani a bayaninsa ya ce ba wata doka ta Najeriya da ta bayar da damar nuna zaman shari’a ta talabijin saboda haka suka yi watsi da ita.

A bukatar da bangarorin ‘yan hamayyar suka shigar daban-daban sun nuna cewa nuna shari’ar ta talabijin abu ne da ya zama dole saboda sha’awar da jama’a ke da ita a kai da kuma damuwar da aka nuna a kan sakamakon zabe shugaban kasar na ranar 25 ga watan Fabarairun 2023.

BBC Hausa

About the author

Muhammad Sani Abdulhamid

Leave a Comment