Abdul Tech Systems Ltd
Labarai

Matukar Ban Tsaya Takara Ba Naci Amanar ‘Yan Najeriya – Osinbajo

Published by Zainab Sabitu

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce ya ci amanar kasa idan bai tsaya takarar mukamin shugaba kasa ba a shekarar 2023.

Mista Osinbajo ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin wata ziyara da ya kai jihar Ondo, kuma ya gana da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu da masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyar APC.

Ya kuma ce rike mukamin mukaddashin shugaban kasa da ya yi a wasu lokuta ya ba shi kwarewar da yake bukata domin ya jagoranci Najeriya.

“Mutane na mutuwa a kowace rana, saboda haka zai kasance cin amanar kasa idan na yi ritaya kuma na koma Legas ko Ikenne bayan wa’adin mulkinmu. Ban yi wa kasar nan adalci ba,” in ji Osinbajo.

A nasa bangaren, Gwamna Akeredolu ya ce duk da cewa ‘yan deleget na jihar suna son sa kuma suna mutunta shi, ubangiji ne kawai ke bayar da mulki.

Osinbajo ya sanar da aniyarsa ta neman mukamin shugaban Najeriya a ranar 11 ga watan Afrilu, kuma tun ranar yake kai ziyara sassan kasar yana neman goyon bayan ‘yan kasar.

🤞 Don’t miss any Article!

We don’t spam! Read more in our Privacy Policy.

Oh hi there 👋
Don't miss anything.

Sign up to receive awesome content in your inbox.

We don’t spam! Read our Privacy Policy for more info.

About the author

Zainab Sabitu

I'm who I am and that's just enough.
I'm definitely the best of my kind.
Just take a seat and grab a cookie.

Leave a Comment