Labarai

Mutane 10 sun mutu a Afrika ta Kudu sakamakon bullar cutar amai da gudawa

 

Hukumomin lafiya sun ce barkewar cutar kwalara ta kashe mutane akalla 10 a lardin Gauteng mafi yawan jama’a a ƙasar Afirka ta Kudu.

Akalla mutane 95 ne tun a ranar Litinin din da ta gabata suka ziyarci asibitocin yankin bayanda suka nuna alamun cutar kwalara a Hammanskraal, wani yanki da ke arewacin babban birnin ƙasar Pretoria.

Gwajin da aka yi a ranar Lahadi ya tabbatar da cewa akalla mutane 19 ne suka kamu da cutar kwalara, in ji ma’aikatar lafiya ta Gauteng a cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta kuma kara da cewa an kwantar da mutane 37 a asibiti wadanda ke cikin mawuyacin hali.

Wadanda abin ya shafa sun hada da yaro dan shekara uku da kuma manya tara.

Shugaban hukumar kula da lafiya na lardin Nomantu Nkomo-Ralehoko, ya bukaci jama’a da su kara daukar matakan kariya da kuma kula da tsaftar hannu.

Birnin Tshwane na gargadin mazauna Hammanskraal da kewaye da kada su sha ruwan famfo, inda ya kara da cewa za’a samar da tankunan ruwa.

Leave a Reply