Siyasa

NNPP Ta Yi Tir Da Rufe Ofishinta A Borno

Jam’iyyar NNPP ta yi Allah wadai da rufe ofishinta na birnin Maiduguri da Hukumar Raya Biranen Jihar Borno ta yi a ranar Alhamis.

A ranar da ta gabata ce dai rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta yi wa harabar ofishin jam’iyyar NNPP da ke Maiduguri kawanya, bisa zargin karya tsare-tsaren birane da ci gaban jihar.

Sai dai daukar wannan matakin ya jawo fushin shugabannin jam’iyyar NNPP, inda suka yi Allah-wadai da lamarin, suna masu bayyana shi a matsayin abin ban takaici.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai ziyarci jihar domin kaddamar da ofishin a karshen mako.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a Maiduguri, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Borno, Abdu Umar, ya ce: “Mun samu korafi daga Hukumar Tsarawa da Ci gaban Birane ta Jihar Borno (BOSUPD) cewa ofishin jam’iyyar na nan a wata unguwa.”

Ya kara da cewa, mayar da gine-ginen gidaje zuwa ofisoshi yana kawo rashin zaman lafiya ga jama’a da kuma karya tsare-tsaren gine-ginen jihar, inda ya ce an dauki matakin ne domin dakile rikici.

Kwamishinan ‘Yan sandan, ya kuma musanta rade-radin da ake yadawa na cewa, ’yan sanda sun kama Mohammed Attom dan takarar Sanatan Borno ta Tsakiya na Jam’iyyar NNPP tare da tsare shi har na tsawon lokaci.

Tuni dai gwamna Babagana Zulum ya umarci Hukumar Raya Birane ta jihar da ta gaggauta bude ofishin jam’iyyar NNPP nan take.

Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da fitar a ranar Juma’ar nan.

Zulum ya ce ko ma mene ne dalilin daukar matakin bai kamata a rufe ofishin a wannan lokaci ba.

Cikin sanarwar, Malam Isa Gusau, ya ce dama al’ummar jihar na da masaniya a kan cewa tun shekaru uku da suka wuce hukumar raya biranen jihar ke daukar matakan kawo gyara ciki har da rufe wasu gine-ginen musamman wadanda ba a yi su bisa ka’ida ba.

Hukumar raya biranen ta ce ta dauki matakin rufe ofishin ne saboda rashin bin ka’idar da ta dace wajen bude ofishin.

Zulum ya ce sake bude ofishin abu ne da kowa zai so sannan kuma yana da kyau a ba wa kowacce jam’iyya dama gudanar da ayyukanta ba tare da wata matsala ba.

Aminiya ta ruwaito yadda hukumar ta rufe hedikwatar NNPP a ranar Alhamis tare da cafke wani dan takarar Sanata na jam’iyyar.

Bayan rufe ofishin dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ta NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Allah-wadai da rufe hedikwatar jam’iyyar da aka yi.

A cikin wata sanarwa da Kwankwason ya fitar a shafinsa a Twitter, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankali da kuma bin doka da oda.

Leave a Reply