Labarai

Boris Johnson Ya Isa Kigali Taron Commonwealth

Firanministan Burtaniya Boris Johnson ya isa birnin Kigali na Rwanda don halartar taron kasashen Commonwealth.

Kafin ya bar Landan, Johnson ya kare shirin gwamnatinsa na tura masu neman mafaka zuwa Rwandar.

Ya kuma ce halartar taron dama ce gare shi ta karfafa dangantakar da za ta yi kyakkyawan tasiri ga kasashen biyu.

Ana sa ran taron na Commonwealth zai mayar da hankali ne kan cinakayya, da habaka hanyoyin samar da abinci, da sauyin yanayi, daa kuma karfafa wa mata da yan mata neman ilimi.

Burtaniya na ci gaba da shan suka kan shirinta na tasa keyar masu neman mafaka kasar zuwa Rwanda.

Ko a makon da ya gabata sai da wata kotu ta hana jirgin da ke dauke da sawun farko na masu neman mafakar tashi zuwa Kigali.

Leave a Reply