Labarai

Kwastam ta kama fatun jaki 1,080 a Kebbi 

 

Hukumar Kwastam ta Kasa ta ce jami’anta sun kama fatun jaki kimanin guda 1,080 a kauyen Geza da ke Karamar Hukumar Dandi a Jihar Kebbi.

Jami’an sun kuma sami nasarar kama wasu miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai kimanin Naira miliyan 94 a Jihar.

Kwanturolan hukumar na shiyyar Birnin Kebbi, Ben Oramalugo, ne ya sanar da hakan lokacin da yake mika kayayyakin ga Kwamandan hukumar a Jihar, Sule Usman.

Ya kuma ce sun kama kulli 371 na tabar wiwi a kusa da kauyen Kawara da ke bakin ruwa a Karamar Hukumar Zuru ta Jihar.

Ben ya ce sauran kayayyakin da suka kama sun hada da dilar gwanjo guda 16 da buhu 37 na shinkafa ’yar waje da kuma litar man fetur 300.

Kwanturolan ya ce darajar kudin kayan ta kai haura Naira miliyan 164, yayin da kwayoyin da aka kwace suka kai na Naira miliyan 94.

Ya ce tuni ma sun kama wani mutum da ake zargi da hannu a safarar kulli 50 na tabar wiwi.

Jaridar Aminiya

About the author

Muhammad Sani Abdulhamid

Leave a Comment