Labarai

Majalisar wakilai na binciken yadda aka kashe kuɗin tallafin Korona

Majalisar wakilan Najeriya ta bai wa akanta-janar na ƙasar zuwa ranar juma’a, ya gabatar mata da cikaken bayanin yadda aka kashe sama da naira biliyan 100 na tallafin yaki da cutar korona, ko ya fuskanci fushinta.

Mataimakin shugaban kwamitin watsa labarai da wayar da kan jama’a na majalisar wakilan, Hon. Salisu Yusuf Majigiri ya shaidawa BBC cewa Majalisar ta yi iya bakin ƙoƙarin ta wajen samun waɗannan bayanai, sai dai ba ta samu haɗin kai daga ofishin akanta-janar ɗin ba.

Ya ce ‘‘akwai biliyoyin kuɗin waɗanda ake ganin sun salwanta a wannan tsakani, kuma amfanin kuɗin shi ne a tallafi rayuwar al’ummma da suka shiga wani hali a wannan tsakani na 2020 zuwa 2022’’

Ya yi bayanin cewa majalisar ta buƙaci bayanai daga akanta-janar ne saboda shi ne ke sane da lissafin duk wani abu da ya shafi dukiyar ƙasa, don haka ita majalisa shi ne tushen fara aikin ta don tantance ‘’mai ya shigo, mai ya fita, kuma da ya fita ina ya je’’

‘‘Kuɗi ne rukuni daban-daban, akwai wanda ake zargin wajen biliyan ɗari kuma akwai wasu daban. Wannan dai ƙadan ne daga cikin abubuwan da aka gabatarwa majalisa don bincike, kuma sakamakon binciken ne kaɗai zai tabbatar da gaskiyar lamarin’’

‘Akwai ayar tambaya kan kudaden tallafin korona a Najeriya’

Hon. Salisu ya ce kwamitin zai yi duk abin da ya dace don ganin an gudanar da sahihin bincike da nbazari game da yadda aka kashe kuɗin, sannan ya yi kira ga sauran hukumomin gwamnati su ƙara zage damtse don bai wa majalisar goyon baya a ƙoƙarin ta na tabbatar da gaskiya kan wannan batu.

Majalisar dai tana zargin cewa an karkatar da kuɗaɗen tallafin korona a ma’aikatu da hukumomin gwmanati, lamarin da ta ce ya ruruta matsalar da jama’ar Najeriya suka fuskanta a lokacin annobar.

A halin yanzu dai majalisar ta riga ta nemi a gabatar mata da dukkan bayanan da takardun shaidar yadda aka kashe kuɗin, a ranara Juma’a, kuma ta sha alwashin ɗaukar matakin ladabtarwa idan har wa’adin ya cika ba tare da an aikata umarnin nata ba.

About the author

Muhammad Sani Abdulhamid