Siyasa

Peter Obi Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra Peter Obi ya bayyana janyewar sa daga takarar shugabancin Najeriya a karkashin Jam’iyyar PDP da kuma ficewa daga cikin ta kasa da sa’oi 72 kafin gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Rahotanni sun ce Obi wanda ya marawa Atiku Abubakar baya a zaben shekarar 2019 ya rubuta wasikar ficewar sa daga Jam’iyyar ce ga shugaban ta Iyorchia Ayu ba tare da gabatar da dalilan daukar wannan mataki ba.

Wasikar ta bayyana cewar Obi ya gabatar da aniyar sa ta janyewa daga PDP kamar yadda doka ta tanada wajen shaidawa shugaban mazabar sa dake Agulu ta 2 a Anaocha ta Jihar Anambra daga ranar 20 ga watan Mayu, matakin da ya kawo karshen aniyar sa ta tsayawa takarar shugaban kasa a Jam’iyyar.

Tsohon gwamnan wanda ya bayyana aniyar sa ta bada gudumawa wajen gina kasa, yace halin da ake ciki yanzu ba zai bashi damar yin haka ba ta hanyar da ta dace, duk da yake babu abinda ya sauya a shirin sa na bada gudumawa wajen ceto Najeriya.

Sai dai Daraktan yakin neman zaben sa Doyin Okupe ya tabbatar da cewar Obi zai tsaya takaran zabe mai zuwa ba tare da bayyana jam’iyyar da zai koma ba.

Leave a Reply