Education Labarai

‘Yajin Aikin Malaman Jami’a Ta ASUU Ka Iya Janyo Babbar Masifa Ga Najeriya

Published by Abdullahi Yahaya

Kungiyar tsofaffin daliban jami’i’on gwamnatin Najeriya, ta yi gargadin cewa yajin aikin da kungiyar malaman jami’a ta ASUU ke yi ka iya zama babban bala’i ga kasar.

A wata wasika da kungiyar ta fitar a ranar Litinin, ta yi kira ga gwamnati da ASUU su sake zama teburin sulhu domin magance matsalar.

Sama da watanni shida kenan da ASUU ta tsunduma yajin aiki a daukacin Najeriya, ko da yake wasu gwamnatocin jihohin Najeriya sun kira malamai su koma bakin aiki, idan ba haka ba babu mai biyansu albashi.

Malaman Jami’o’in na bukatar a kara musu albashi, da alawus-alawus da sauran bukatu.

Daya daga cikin abubuwan da ke kara tunzura yajin aikin shi ne, rashin biyan jami’o’i kudaden shiga da suka kai sama da Naira Tiriliyan 1.

About the author

Abdullahi Yahaya

Seasoned Blogger. Software Developer. Web Designer & Developer. Cybersecurity Expert. Database Engineer. IT Enthusiast.

Leave a Comment