LabaraiTrending

Zaftarewar kasa ta yi ajalin wasu mutane a Kamaru

 

Zaftarewar kasa da ta biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya na sa’o’i sama da hudu ta kashe akalla mutum goma sha biyar a birnin Yaounde na kasar Kamaru.

Iftila’in da ya auku a unguwar Mbankolo ranar Lahadi ya rutsa da gidaje 25 kamar yadda gidan rediyon gwamnatin Kamaru ya ambato jami’ai yana cewa.

Rahotanni sun ce ruwa ya mamaye kan tituna, lamarin da ya hana ‘yan kwana-kwana kai dauki ga mutanen da lamarin ya rutsa da su cikin sauki.

Rahotannin sun ce cikin dare ne lamarin ya auku, kuma mutanen gari ne suka fara kai wa mutanen da abin ya shafa dauki.

Ko a watan Nuwamban bara zaftarewar kasa ta kashe mutum 14 a babban birnin kasar ta Kamaru.

A ranar Lahadi an yi gargadin cewa za a yi ambaliyar ruwa a wasu jihohin kasar Nijeriya da ke makwabtaka da Kamaru sakamakon sakar ruwa daga wata madatsar ruwa a Kamaru.

TRT Afrika