Labarai

Uwa Ta Sayar Da Jaririnta Naira Dubu 600 A Ogun

Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta cafke wata mata, mai shekaru 23 (an sakaya sunanta), wacce ake zargi da sayar da jaririnta ɗan sati uku kacal da haihuwa a kan kudi N600,000.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta a yau Alhamis.

Oyeyemi ya ce an kama matar ne a ranar 18 ga watan Agusta, biyo bayan korafin da mahaifin jaririn ya yi a shelkwatar ‘yan sanda ta Mowe da ke Ogun.

Oyeyemi ya ce mahaifin jaririn ya ba da rahoton cewa yana soyayya da wacce ake zargin, sai ta samu juna biyu kuma ya kama mata hayar wani gida da take zaune har ta haifi yaron.

“Ya bayyana cewa wacce ake zargin ba zato ba tsammani tare da jaririn daga gidan makonni uku bayan haihuwa, sai aka neme ta a ka rasa, inda garin bincike, a ka gano ta a wani otal ta na sharholiyar ta da wani mutum.

“Duk kokarin da aka yi na sanin inda jaririn ya ke ya ci tira,” in ji Mista Oyeyemi.

Ya ce jami’in ‘yan sanda na reshen Mowe, SP Folake Afeniforo, ya yi cikakken bayani kan jami’an da suka gudanar da bincike a wurin kuma an kama wacce ake zargin.

Oyeyemi ya ce, da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa ta sayar da jaririn ne a kan Naira 600,000 ga wani a jihar Anambra.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa wadda ake zargin ta ce kawarta ce ta kai ta wajen mai saye kuma suka raba kudin daidai-wa-daida.

A cewar kakakin, an kama kawar kuma ta tabbatar da ikirarin matar.

Leave a Reply