Abdul Tech Systems Ltd
Labarai

‘Yan bindiga sun sace amarya a hanyar kai ta gidan miji a Neja

Published by Abdullahi Yahaya

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wata amarya a kan hanyar kai ta gidan angonta a jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta ce ‘yan bindigar sun bayyana ne a lokacin da ‘yan uwa da abokan amaryar ke hanyarsu daga kauyen Allawa na karamar hukumar Shiroro zuwa gidan angon nata a garin Fandogari na karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Rahotanni sunce maharan da ke da matukar yawa sun yi wa ayarin amaryar kwanton bauna ne a ranar Juma’a a kan hanyarsu, inda suka dauke amaryar. Da sauraan wadanda ke cikin motar.

Wasu majiyoyi sun ce ‘yan bindigar, wadanda suka yi awon gaba da dimbim shanu, sun kuma kai hari a kauyen Gyaramiya a karamar hukumar shiroron har ila yau, inda suka sace dimbim mazauna kauyen.

Kokarin samun kakakin ‘yan sandan jihar don karin bayani ya ci tura.

Ba wannan ne karo na farkko da ‘yan bindiga ke karkata akalar amarya a kan hanyarta ta zuwa gidan angonta ba.

SourceRFI Hausa

🤞 Don’t miss any Article!

We don’t spam! Read more in our Privacy Policy.

Oh hi there 👋
Don't miss anything.

Sign up to receive awesome content in your inbox.

We don’t spam! Read our Privacy Policy for more info.

About the author

Abdullahi Yahaya

A PRO Blogger. A Web Designer and Developer. A Publisher. A Database Engineer. A Social Media Strategist. & an IT Enthusiast.

Leave a Comment