Siyasa

Zulum Ya Sa A Rufe Ofishin Mu A Borno – NNPP

Ofishin yakin neman zaben Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi zargin cewa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ne ya umarci ƴan sanda a jihar da su rufe sakatariyar jam’iyyar gabanin ziyarar da dan takarar shugaban kasa, Rabi’u Kwankwaso zai kai a ranar 27 ga watan Agusta.

A wata sanarwa mai taken “Gwamnatin jihar Borno ta rufe shelkwatar NNPP da ke Maiduguri da karfi da yaji” mai ɗauke da sa hannun Muyiwa Fatosa, NNPP ta ce ‘yan sandan ba kawai sun rufe harabar ba kaɗai, sun lalata kayan aiki tare da dukan ma’aikata.

“Da safiyar yau ne tawagar jami’an tsaro karkashin MOPOLS ta rundunar ‘yan sandan Najeriya suka rufe shelkwatar mu ta ƙarfi-da-yaji, inda suka lalata kayayyakin aiki, suka kuma raunata tare da fatattakar gungun ma’aikata da ‘yan jam’iyya da magoya bayansu.

“Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma dan takarar shugaban kasa, Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso, PhD FNSE ya kai ziyara jihar Borno a cikin kwanaki biyu, Asabar 27 ga watan Agusta, 2022.

“Ku tuna cewa Gwamna Kwankwaso yana zagayawa a fadin kasar nan inda ya kaddamar da ofisoshin jam’iyyar NNPP, ya ke kuma ci gaba da samun goyon bayan jama’a da dimbin magoya bayansa cikin lumana kuma har a jihar Borno ma.

“Ba za mu taba yarda da wannan mataki ba kwata-kwata kuma muna Allah-wadai da shi gaba daya. Wannan a zahiri yana nuna wata mummunar alama ce nan gaba yayin da muke tunkaro ruguntsimin yakin neman zaɓe.

“Don haka muna kira ga gwamnatin jihar Borno da ta buɗe mana ofishinmu ta kuma umarci jami’an tsaro da ke bakin sakatariyar mu da su ɓace daga harabar mu.

“Dole ne ‘yan sanda da jami’an tsaro su bijirewa duk wani yunƙuri na yin amfani da su a matsayin makami daga wasu ‘yan siyasa masu son tada zaune tsaye,” in ji shi.

Leave a Reply