Latest:
Labarai

Ƴan Boko Haram sun kashe manoma 7 a Borno

Mayaƙan jihadi a yankin Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun kashe aƙalla manoma bakwai a wani ƙauye da ke kusa da birnin Maiduguri.

Shugabannin mayaƙan sa-kai da jami’ai na cewa mayaƙan na Boko Haram sun kashe manoman ne ta hanyar fille musu kawunan a ranar Alhamis.

Gwamnatin Borno na ta fito da tsare-tsaren mayar da mutanen da Boko Haram ta raba da matsugunansu, garuruwansu da karfafa musu giwuwar komawa gonaki.

Sai dai Boko Haram da abokiyar hamayyarta Iswap sun tsaurara hare-hare kan manoma a wannan lokaci.

BBC Hausa

Leave a Reply