Labarai

Ƴan Najeriya 23,000 sun yi ɓatan-dabo saboda matsalar tsaro cewar Gwamnatin Tarayya

 

A jiya ne gwamnatin tarayya ta ce, a kalla ‘yan Nijeriya dubu ashirin da uku (23,000) ne suka yi batan dabo da har yanzu ba gansu ba sakamakon matsalolin da suka shafi ayyukan ta’addanci, garkuwa da mutane da sauransu.

Ministan jin kai da rage kaifin radadin fatara, Betta Edu, ita ce ta shaida hakan a ranar bikin tunawa da wadanda suka bata na duniya ta shekarar 2023 a hukumar kare hakkin bin-adama, ta ce, adadin wadannan mutanen da suka batan har yanzu ba a san inda suke ba.

Edu, wacce ta samu wakilcin daraktan harkokin jin kai, Ali Grema, ta ce, akwai bukatar a kara muhimmanta hanyoyin da ake bi wajen bada rahoton wadanda suka bace da matakan da ake bi wajen bibiyarsu domin rage kaifin mutanen da suke salwantuwa.

“A Nijeriya, kasa da shekara goma, sama da mutum 25,000 ne hukumar ICRC da Nigerian Red Cross Society (NRCS) ne suka yi rijistan bacewarsu sakamakon matsalar tsaro a arewa maso gabas. Wannan kwatankwacin rabin mutanen da suka bace kenan a nahiyar Afrika gabaki daya.

“Zuwa yau, sama da mutum 23,000 har yanzu sun bace bat. Akwai bukatar kara kokari kan bada rahoton wadanda suka bace da sabunta hanyoyin bibiyar sawun wadanda suka bace. Zuwa yanzu, adadin mutanen da suka bace din ba a iya gano su ba,” Edu ta shaida.

Jaridar Leadership Hausa

Leave a Reply