Labarai

Ƴan Najeriya za su iya zuwa Dubai Yanzu

 

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta cire haramcin biza a kan ‘yan Najeriya, kamar fadar shugaban Najeriya ta bayyana.

Wata sanarwa daga fadar shugaban ta United Arab Emirates (UAE) ta ɗauki matakin ne bayan ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da takwaransa Mohamed bin Zayed Al Nahyan a yau Litinin a birnin Abu Dhabi.

“Kazalika, wannan yarjejeniyar na nufin kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na Etihad da Emirates za su ci gaba da shiga da fita a Najeriya nan take,” in ji sanarwar da Ajuri Ngelale ya fitar.

Ta ƙara da cewa yarjejeniyar ba ta ƙunshi biyan wani kuɗi ba a nan kusa tsakanin ƙasashen, yana mai nuni da miliyoyin dalolin da gwamnatin Najeriya ta riƙe wa kamfanonin jiragen na kuɗin tikiti.

Kusan shekara ɗaya ke nan da UAE ta dakatar da bai wa matafiya daga Najeriya biza, a rikicin da ya samo asali tun daga lokacin annobar korona.

BBC Hausa

Leave a Reply