Labarai

Ƴan Sanda sun tabbatar da sace dalibai mata 4 a Zamfara

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Zamfara ta tabbatar da sace wasu ɗalibai mata huɗu na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tsafe.

Kakakin rundunar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN, a Gusau a yau Laraba.

Shehu ya ce an yi garkuwa da daliban ne a daren ranarTalata.

“Wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a dakin kwanan dalibai da ke wajen makarantar, wani gidan haya a garin Tsafe.

“Da samun rahoton, jami’an tsaro sun fatattaki masu garkuwa da mutane, daya daga cikin daliban biyar da aka sace ta tsere daga hannun ƴan bindigar amma kuma sun gudu da sauran hudun,” in ji Shehu.

Kakakin ya ƙara da cewa rundunar ta kai jami’an ta na sashin nema da kubutarwa domin haɗa kai da sojoji don a tserar da ɗaliban.

Leave a Reply