Labarai

AFCON 2023: Super Eagles ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin Afirka

 

Tawagar kwallon kafar Nijeriya ta Super Eagles ta yi nasarar samun gurbin zuwa gasar cin kofin Nahiyar Afirka ta 2023 wato Africa Cup of Nations (AFCON).

Tawagar ta yi nasara ne bayan ta doke tawagar kwallon kafar Sierra Leone da ci 3 -2 a wasan da suka yi a filin Samuel Kanyon Doe da ke Monrovia, kasar Liberia, ranar Lahadi.

Sai dai har yanzu tawagar tana da sauran wasa guda da za ta fafata.

TRT Afrika Hausa

Leave a Reply