Latest:
Labarai

Alhazan Najeriya 13 sun Mutu a Saudiyya 

 

Alhazan Najeriya da suka mutu a aikin hajjin 2023 ya kai 13 a daidai lokacin da wasu 41,632 a’ke duba lafiyansu a kasar ta Saudiyya.

Shugaban tawagar likitocin Najeriya mai kula da mahajjata, Dr Usman Galadima ne ya bayyana haka a birnin Makkah yayin taron duba lafiyar alhazai bayan aikin Arafat.

Ya ce tawagarsa sun duba marassa lafiya maniyyata dubu 25,772 a lokacin Zaman Muna da Arafat baya ga 15,680 da dasuka karbi magani a Madina da Makka a lokacin shirin aikin ranar 09 ga Zhul-Hajj.

Galadima ya gano cewar alhazai bakwai ne suka rasu yayin aikin Arafat wanda Plateau keda 1, Kaduna 2, Osun 2, Borno 1, Yobe 1, Birnin Abuja 1, Benue 1 da kuma Legas mai mutum 1, yayin da Wani rahoto yayi nuni da mutuwar mutane uku.

Galadima yace yayin aikin Arfat Alhazai hudu sun rasa rayukansu kana biyu suka rasu a minna.

Yace sun sami rahoton matsaloli 93 Inda aka basu agajin gaggawa ciki kuwa har’da matsalar ciwon kai,sai mutum 12 dasu Zazza6in cizon sauro ya damesu da dai sauran su.

Yakara da cewar yawancin mahajjatan sun sami rashin kwarin gwiwa yayin fita zuwa jifar shedan.

Komishinan hukumar jin dadin alhazai na kasa wato NAHCON mai kula da zirga-zirgan jiragen sama,Goni Sanda ya bayyana cewar za’a fara jigilar alhazan Najeriya a’ranar 4 ga watan Yuli zuwa ranar 3 ga watan Augusta.

Leave a Reply