Labarai

An Fitar Da Sunayen Mutane Mafi Arziki A Afirka A 2022

Attajiran Afirka sun fi arziki yanzun fiye da yadda suke a shekarun baya, duk da barkewar cutar korona a duk duniya. A rukuni wadanda suka mallaki biliyoyi, mutum 18 na nahiyar suna da dukiya darajar dalar Amurka dala biliyan 96.5 daga 2014.

Alike Dangote na Nijeriya shi ne attajirin da ya fi kowa arziki a Nahiyar, wanda ya kai dalar Amurka biliyan 13.9, a bara yana da sama da dala biliyan 12.1, sakamakon karuwar kashi 30 cikin 100 na farashin hannayen jarin Simintin Dangote, kadararsa mafi daraja.

Ya tsallaka zuwa matsayi na 2 daga na 4 a bara – shine mai kayan ado, Johann Rupert na Afirka ta Kudu. Ya samu riba fiye da kashi 60 cikin 100 na farashin hannun jari na Compagnie Financiere Richemont – mai yin agogon cartier da alkalami na Montblanc – kamfanin ya tura dukiyarsa zuwa dala biliyan 11, daga dala biliyan 7.2 a shekara da ta gabata.

Nicky Oppenheimer dan kasar Afirka ta Kudu, wanda a baya ya mallaki kamfanin hakar lu’u-lu’u DeBeers kafin ya sayar da shi ga kamfanin hakar ma’adinai na Anglo American shekaru goma da suka gabata, yana matsayi na 3, wanda ya kai kimanin dala biliyan 8.7.

Strive Masiyiwa na Zimbabwe, wanda ya kai dalar Amurka biliyan 2.7, a bara yana da dala biliyan 1.2. Hannun jarin Econet Wireless Zimbabwe, da ya kafa, ya karu da sama da kashi 750 cikin 100 a cikin shekarar da ta gabata, wanda ya taimaka wajen kara girman arzikinsa.

Sai Attajirin nan na Nijeriya Abdulsamad Rabiu, wanda ya kai sama da dala biliyan 1.5

SourceLeadership Hausa

Leave a Reply