A Jamhuriyar Nijar, an rufe makarantu 890 a cikin gundumonin kasar 14 na jihohi hudu da ke fama da matsalolin tsaro.
Jihohin da wannan matsala ta shafa sun hada da Tillabery da Diffa da Tahoua da kuma Maradi.
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF tare da hadin gwiwar ma’áikatar illimi ta kasar da kuma kungiyar da ake kira Closter Education Niger, ne suka fitar da wannan kiyasi.
A watan Augusta kadai, bincike ya gano cewa an rufe makarantun firamare 855 da na sakandire 35 a gundumomi 14 na jihohin kasar hudu saboda dalilai na tsaro.
Tuni dai gwamnatin kasar ta ce ta dauki matakai musamman a Tilabery don shawo kan matsalolin tsaro da kuma nazari a kan matakan da za a dauka don ganin yaran da lamarin ya shafa sun koma karatu.
To amma kungiyar muryar talaka ta bakin shugabanta Alhaji Nasiru Sa’idu,ya ce duk da matakan da gwamnatin ta ce za ta dauka don magance tsaro, akwai bukatar a kuma samar da malamai na musamman da za su taimaka wa yaran wajen daidaita karatun su.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.