Labarai

An tsinci jariri a cikin gona a Jigawa

 

An tsinci wani jariri sabuwar haihuwa a cikin gonar wani Bafulatani a Karamar Hukumar Gwaram da ke Jihar Jigawa.

Bafulatanin mai suna Dubore, ya tsinci jaririn ne a cikin kwali a yayin da yake tsaka da aiki a gonarsa da safiyar wannan Lahadi.

Ganin haka Dubore ya garzaya Fadar Dagacin yankin Wurya da ke tsohowar Gwaram game domin shaida masa lamarin.

Bayan ganin abin da ya faru Dagacin mai suna Malam Aminu Abdul-hamid ya kira hadimin Shugaban Karamar Hukumar Gwaram Alhaji Tamaji Gwaram domin daukar mataki.

Tamaji Gwaram ya ce sun kai jaririn wajen Batauren Dan Sanda na Karamar Hukumar, inda nan take aka kai jaririn asibiti domin bincikar lafiya sa wanda aka same shi cikin koshin lafiya.

Yahaya Tamaji ya ce daga bisani suka kai jaririn wajen Shugababan Karamar Hukumar Honorabil Zaharadden Abubakar inda ya ba da umarnin nemo wadda za ta shayar da shi.

Cikin nasara a cewar Hadimin Shugaban Karamar Hukumar mai dakin Dagacin Wurya mai suna Amina Aliya da yake tana shayarwa ta karbi jaririn domin kulawa da shayar da shi.

Tamaji ya ce shugaban karamar hukumar ya sa an rada wa jaririn suna kuma aka yanka masa rago.

Wakilinmu ya ruwaito cewa yanzu haka jaririn ya samu iyaye wanda kuma aka rada masa Zaharadeen Aminu.

Dagan nan a cewar Tamaji, shugaban karamar hukumar ya sanya wa mai shayarwar alawus din naira dubu ashirin duk wata da ba ta tallafi har zuwa karashen wa’adin mulkin sa na karamar hukumar.

Daga bisani Aminya ta kara tuntubar kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam kuma ya tabbatar da lamarin