Home Labarai Atiku ya bukaci Kotun koli tayi watsi da bukatar Tinubu kan takardun...

Atiku ya bukaci Kotun koli tayi watsi da bukatar Tinubu kan takardun bogi

 

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci Kotun Koli ta yi watsi da bukatar Shugaba Tinubu na kin karbar sabbin hujjojin Atikun kan zargin Tinubun da amfani da takardun bogi.

Atiku ya gabatar da sabbin hujjoji ga Kotun Kolin kan zargin amfani da takardun bogi da yake cewa Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu da Tinubun ya lashe.

Ya ce amfani da takardun bogin da Tinubu ya yi domin rike matsayi mafi girma a Najeriya na da matukar hatsari bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka ya kamata a taka masa burki.

A kan haka ne ya nemi Kotun Kolin da ta yi watsi da bukatar Tinubu na kin karbar sabbin hujjojin bisa hujjar sarkakinar da za su haifar a shari’ar.

Lauyan Tinubu, Wole Olanipekun (SAN) ya shaida wa kotun cewa maganar takardun shaidar karatu batu ne da ya danganci abubuwan kafin zabe, don kotun ba ta da hurumin karbar sabbin hujjoji a kansu.

Amma lauyan Atiku, Chris Uche (SAN)  ya bayyana cewa rashin karbar hujjojin ne zai haifar da karin sarkakiya, don haka ya ce karbar karin hujjojin zai tabbatar da cikakken adalci a shari’ar, “don gano gaskiyar zargin amfani da takardun bogin ko akasin haka.”
Jaridar Aminiya

Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.