Labarai

Ba Zamu Kara Farashin Kaya A Lokacin Azumi Ba – Abdussamad BUA

Shugaban rukunin kamfanin BUA Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabiu ya yi wa ‘yan Nijeriya alkawari cewa ba zasu kara farashi wa kayan kamfaninsu ba, musamman yadda watan azumin Ramadan ya gabato.

Mai wakilta Shugaban kamfanin a yanki Arewa Alhaji Muhammadu Adakawa ya shaida hakan a yayin hirarshi da manema labarai a birnin Kano. Adakawa ya bayyana cewa Shugaban kamfanin ya bukaci su sanar wa ‘yan Nijeriya cewa ba zasu kara farashin kayansu ba.

Adakawa ya bada misalin yadda wasu kamfanoni suka kara kudin sukarin su zuwa Naira 1500, ya ce kamfaninsu ba zai yi irin hakan ba.

SourceLeadership Hausa

Leave a Reply