Siyasa

Bance Zan Mika Jami’o’in Najeriya Wa Jihohi Ba

Dan takarar shugaban kasa a Najeriya karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya musanta rahoton da ke ikirarin cewa zai mika jami’o’in kasar a hannun jihohi da zarar an zabe shi don jagorantar kasar a zaben 2023.

A wata sanarwa da mashawarcin dan takarar kan harkokin yada labarai Mazi Paul Ibe ya fitar ta bayyana cewa kafofin yada labarai basu fahimci hakikanin kalaman abin da Atiku Abubakar ya ke nufi a cikin kalaman nasa ba.

Jaridun Najeriya sun ruwaito, Atiku na shaidawa taron kungiyar lauyoyin kasar cewa daya daga cikin manufofin da ya tsara zai aiwatar idan an zabe shi, shine sakin mara ga bangaren yan kasuwa wadanda suke cikin gida da kasashen ketare, saboda gwamnatin tarayya bata da kudaden gudanar da kowanne aiki.

Sai dai sanarwar ta Mazi Paul Ibe ya ce sam kafofin basu fahimci abin da dan takarar na PDP ke fadi ba, maimakon haka sai suka fitar da kalaman da basu ne ya ke nufi ba.

A cewar sanarwar Atiku Abubakar na nufin zai gabatar da wani sabon shirin karkashin tsarin ilimin Najeriya da za ta rarraba karfin ikon sashen ilimi zuwa rukunnai don rage ikon bangare guda.

Sanarwar ta jaddada manufar Alhaji Atiku Abubakar ta sanya ilimi a kan gaba da zarar aka zabe shi matsayin shugaban kasa tare da kawo sabbin shirye-shiryen da za su bunkasa harkar koyo da koyarwa a sassan kasar.

Leave a Reply