â Daga Muhammad Sani Muazu
Hukumar Kula da Lafiyar Muhalli ta Jihar Bauchi (BASEPA), tare da hadin gwiwar WaterAid International, ta shirya wani taron horo na kwana guda a ranar 27 ga Yuli, 2025, domin karfafa gwiwa da kuma koyar da yadda ake amfani da sabbin kayan aikin zamani wajen gudanar da binciken tsaftar muhalli.
Taron, wanda aka gudanar a Bauchi, ya tattaro jamiâan lafiya da kwararru kimanin 100 daga kananan hukumomi daban-daban a fadin jihar, inda aka mayar da hankali kan sauya hanyar gudanar da binciken tsafta daga tsarin rubuce-rubuce zuwa tsarin zamani ta hanyar amfani da naâurorin kwamfuta da wayoyin hannu.
Manufar horon ita ce samar da ingantaccen tsarin aiki wanda zai rage bata lokaci, inganta sahihancin rahotanni, tare da saukaka bin diddigin ayyukan maâaikata kai tsaye.
Daya daga cikin mahalarta, Hajiya Balkisu Adamu, ta bayyana jin dadinta da wannan horo, inda ta ce canjin ya zo da sauki ga ayyukansu.
“Na koyi yadda zan mayar da aikinmu daga na hannu zuwa na zamani ta amfani da wayar Android. Wannan zai rage mana wahala, saboda a da kullum sai mun yi rubuce-rubuce da yawa. Yanzu kuma za mu iya yin aikin da kuma aika rahoto nan take. Muna godiya matuka ga wadanda suka shirya wannan muhimmiyar horo,” in ji ta.
Shi ma wani mahalarta, Ismaâil Yusuf, ya bayyana cewa lokaci ya yi da ake bukatar bin zamani domin aiki daidai da cigaban fasaha a duniya.
“Ba za mu ci gaba da aiki da tsohuwar hanya ba. Duniya yanzu ta koma kan tsarin zamani, haka kuma binciken tsafta. Zan aiwatar da abinda na koya, saboda a da takarda muke amfani da ita. Amma yanzu an koma tsarin zamani, aikin ya fi sauki. Zamu koma mu wayar da kan abokan aikimu da kuma alâumma game da tsafta da ilimin lafiya,” in ji shi.
Abdulmalik Yusuf daga BASEPA ya ce tsarin zamani zai kawo inganci da gaskiya a fannin binciken muhalli, inda ya ce duk wanda har yanzu ke amfani da tsohuwar hanya, to ya bar baya da kura.
“A da takarda muke amfani da ita wajen fitar da rahoto. Amma yanzu mun koyi yadda ake amfani da tsarin kwamfuta. Wannan zai inganta aikace-aikacenmu. Mun shiga zamanin fasaha, dole mu rungume shi. Wannan tsari zai taimaka wajen bin diddigin jamiâan da ba sa yin aiki yadda ya kamata, saboda duk wani aiki da muke yi ana iya gani kai tsaye a cikin naâura,” in ji shi.
Daraktan Sashen Bincike, Tilasta Bin Doka da Tsabtace Muhalli na BASEPA, Muhammad Usman Saleh, ya ce sauya daga rubuce-rubuce zuwa tsarin kwamfuta wani bangare ne na kokarin tabbatar da cewa an samu sahihan bayanai daga binciken gida-gida.

“Mun bar yin bincike ta hanyar takarda, yanzu muna amfani da waya ko kwamfuta wajen gudanar da bincike. Bayan an kammala, bayanan za su tafi kai tsaye zuwa ga uwar garke domin samun sahihiyar majiya ta bayanai. Mun horas da mutane 100, wadanda suka hada da jamiâan lafiya daga LGAs, BASEPA, da Kwamitin Lafiyar Muhalli na Kasa. Daga kudu mun gayyato mutane biyar, daga Jamaâare hudu, daga Tafawa Balewa uku, sauran kuma sun fito daga sauran sassan jihar,” in ji shi.
Saleh ya bayyana cewa an shirya horon ne domin koyar da mahalarta yadda za su yi amfani da sabon tsarin duba tsafta ba tare da kuskure ba, tare da samun bayanai masu inganci da sahihanci.
Taron horon wani bangare ne na kokarin da ake yi a jihar Bauchi domin inganta tsarin lafiya da tsaftar muhalli ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









