Latest:
Labarai

Buhari Ya Kafa Kwamitin Da Zai Kawo Karshen Yajin Aikin Malaman Jami’a Ta ASUU

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin da zai duba bukatun Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) da nufin kawo karshen yajin aikinta.

Tun a watan Fabrairun bana ne dai kungiyar ta tsunduma yajin aikin saboda yadda ta ce gwamnatin ta gaza cika mata alkawuran da ta dauka a yarjejeniyoyinsu na baya.

Ana tsaka da yajin aikin ne dai Gwamnatin Tarayya ta lashi takobin cewa za ta aiwatar da manufar ‘ba aiki, ba albashi’ saboda ba zai yiwu ta biya su albashin watanni shidan da ba su yi aiki ba.

Sai da malaman sun yi watsi da matakin na gwamnati.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ne ya sanar da matakin Buharin na kafa kwamitin a Abuja ranar Talata bayan kammala taro da Shugabanni da iyayen jami’o’i na Najeriya.

Ministan ya ce kwamitin ya kunshi iyayen jami’a guda hudu da shugabannin jami’a su ma guda hudu, wadanda dukkansu za su kasance a karkashin jagorancinsa.

Kwamitin dai a cewar Ministan, zai duba batutuwan da aka sami sabani a kansu tsakanin malaman da gwamnati.

Adamu ya ce zai tattauna da Buhari bayan kammala taron don shaida masa abubuwan da suka tattauna.

Kodayake bai bayyana lokacin da kwamitin zai fara aiki ba, amma ya ce la’akari da yadda abubuwa suke a halin yanzu, a cikin ’yan kwanaki kwamitin zai fara aiki.

Sai dai ya ce hakan ba yana nufin za su yi watsi da kwamitin Briggs da yanzu haka shi ma yake nasa kokarin shiga tsakanin ba ne.

Tun da farko dai, Ministan ya ce, “Ba zai yiwu gwamnati saboda kawai tana so ta kawo karshen matsalar ta kawo matsalar da za ta gagara warwarewa a nan gaba.”

Minista Adamu ya kuma ce sanarwar da ASUU ta fitar ta bakin shugabanta cewa ba lallai ne ta sake zama da Gwamnatin Tarayya ba a kan batun dole a yi watsi da ita.

Leave a Reply