A kasar kwaddabuwa, akwai wata kabila mai suna Nabankaha, wadda bunsuru ya shekara 15 yana shugabantar al’ummar yankin.
A bisa al’adar al’ummar da ke zaune a kauyen Nabankaha, bunsuru suke nadawa ya shugabanci kabilarsu ta Senoufo, a maimakon dan Adam.
Sunan sarautar sarki bunsurun Bakoroni Mai Daraja ta daya, kuma wanda ke mulki yanzu ya shekara akalla 15 a kan karaga.
Duk da cewa ba dan Adam ba ne, al’ummar kabilar Senoufo da ke kauyen sun ce suna daukar shugaban nasu a matsayin dan Adam, kuma suna daukar sa da matukar daraja.
“Idan da zai rasu, dole mu sake nemo wani daga cikin ’ya’yansa mu nada shi a shugabanmu,” kuma babu wani dan kauyen da ke iya cutar da shi.
Mutanen kauyen sun yi amannar cewa bunsurun da ke jagorantarsu shi ne mai ba su kariya, da kuma gargajiyarsu, wanda a cewarsu, shi ne amfanin sarkin kabila.
Don haka a matsayin shugabansu, babu mai korarsu, ballantana hantarar sa, duk abin da zai yi.
Wani dan kabilar, Emmanuel, Ouattara, ya ce, hasalima, “Muna alfahari da kasancewarsa a cikin wannan al’umma ta Nabahanka.”
Sarkin nasu bunsuru na yawata tare da watayawa ko’ina a wannan masarauta ba tare da wani mutum ko wani abu ya cutar da shi ba.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.