Labarai

Dalibin Jami’ar Gombe Ya Rasu Yana Tsaka Da Rubuta Jarrabawar Karshe

 

Wani dalibin Jami’ar Jihar Gombe da ke zangon karatu na karshe mai suna Abubakar Muhammad, ya rasu yayin da yake tsaka da rubuta jarrabawar kammala makarantar.

Dalibin dai na karatu ne a sashen koyon aikin Akanta na jami’ar.

Wani abokin karatun marigayin ya bayyanawa wakilinmu cewa marigayin ya zo dakin rubuta jarrabawa a ranar sai rashin lafiya ta kama shi inda nan take aka garzaya da shi zuwa cibiyar lafiya ta jami’ar dan duba lafiyarsa.

Sai dai a cewar majiyar, jikin dalibin ya tsananta, amma kafin nan rai ya yi halinsa, inda aka wuce da shi dakin adana gawarwaki a asibiti.

“Ya rasu a cibiyar lafiya ta jami’ar sannan daga bisani mataimakin shugaban sashen tsaro na jami’ar ya jagoranci daukar gawar zuwa dakin adana gawarwaki na asibitin kwararru na Jihar Gombe tare da wasu abokansa da kuma wasu jami’an jami’ar,” in ji dalibin.

Da wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Mohammed Abubakar, ya tabbatar da rasuwar dalibin.

Sai dai ya ce dama dalibin ba shi da lafiya a ranar tun kafin shigarsa dakin zana jarrabawar.

Jaridar Aminiya