Latest:
Labarai

Duk Jami’in Da Ba Shi Da Hurumi A Taron MDD Ba Zai Samu Bizar zuwa Amurka Ba – Tinubu

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar cewa duk wani jami’in gwamnati da ba shi da wani hurumi a taron da Majalisar Dinkin Duniya za ta gudanar a Amurka, ba zai samu bizar tafiya ba.

Kan haka ne Tinubu ya umurci Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya da ta dakatar da aikin ba da biza ga duk jami’an gwamnati da ke neman damar zuwa birnin New York na Amurka don halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya UNGA na bana.

A sanarwar da mai bai wa Shugaban Shawara ta Musamman, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Litinin, shugaban ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan rage yawan kashe kudaden da gwamnati ke yi ne wajen biyan tafiye-tafiye ga jami’anta.

Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunan duk wani jami’in gwamnati da zai je taron ba tare da wata hujja ba ta shiga kai tsaye cikin jadawalin ayyukan UNGA da aka tsara ba.

“Don takaita duk wani tsaiko da ka iya biyo bayan wannan umarni, Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya da ke aikin ba da biza tare da babban ofishin da ke birnin New York, za su yi aiki tare wajen tabbatar da an bi matakan da suka dace wajen tantance wadanda ba sa cikin mutanen da aka ware za su je taron a hukumance,” in ji sanarwar.

Bisa ga wannan umarni na shugaban, an bukaci duk wata ma’aikata ta tarayya da hukumomi su tabbatar da cewa sun takaita yawan jami’ansu da suka saka a cikin tawagar da za su halarci taron na UNGA.

Kazalika Shugaba Tinubu ya bayyana cewa daga yanzu dole jami’an gwamnati su dinga taka tsantsan wajen tafiyar da kudaden al’umma da ake kashewa.

Leave a Reply