Labarai

Ganduje da Soludo sun gamu da cikas yayin shiga wurin manyan baki na alfarma

Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gamu da cikas a bukin rantsar da sabon shugaban kasa a Eagle Square da ke Abuja.

Ganduje da matarsa Hafsat sun yi kokarin shiga cikin wurin da ake kebe wa manyan baki masu alfarma amma sai jami’an tsaro suka dakatar da shi suka ce takardar gayyatar da yake da ita koriya ce kuma sai mai takardar gayyata mai ruwan gwal ne zai shiga cikin wannan bangaren.

Ya jira na tsawon fiye da minti 10 kafin ya dauki kaddara ya koma bangaren da aka tanadar wa baki irinsa.

Shi ma gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya yi kokarin shiga wannan bangaren amma kamar Ganduje shi ma jami’an tsaro sun taka masa birki.

BBC Hausa

Leave a Reply