Shugaban hukumar kare haƙƙin masu sayen kaya ta Kano Janaral Idris Bello Dambazau ya tsere daga hannun jami’an Anti Kwarafshin.
Shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta Kano Barista Mahmud Balarabe ne ya bayyana hakan a yau.
Ya ce, suna gayyaci Dambazau ne kan zargin da ake masa na karɓar cin hanci daga hannun mutane daban-daban.
Ana tsaka da bincike sai ya nemi izni cewa zai je ya sha magani, sai aka haɗa shi da ƴan sanda, daga nan sai ya arce, inji Barista Balarabe.
Balarabe Mahmud ya ce, bai gamsu da bayanan da Dambazau ya yi ba, a don haka za a ɗauki mataki na gaba a kansa.
Freedom Radio dake Kano ta ruwaito cewa ta so jin ta bakin Janaral Dambazau amma bai ɗauki kiraye-kirayen wayar da aka masa ba.
Sannan an aike masa da saƙon karta-kwana amma har kawo lokacin haɗa wannan rahoto babu amsa.
Idan za’a iya tunawa hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta bada umarnin a kamo mata shugaban hukumar kare hakkin masu sayen kaya ta jihar Janar Idris Bello Danbazau mai ritaya kwanakin baya.
Shugaban hukumar Barista Mahmud Balarabe dai shi ya bada umarnin biyo bayan zargin Danbazau da karbar na goro.
“Ni na tura ma’aikata da yan sanda don su gayyato mana shi, kasancewar an akwo mana korafi a kansa, musamman wani mutuum da yayi korafin cewa an kama masa madara kuma an bukaci ya biya kudi kafin a sakar masa kayansa, kuma ya bayar amma ba a dawo masa da kayan ba”.
“Mun tura masa takarda da farko bai amsa ba, inda y ace mana baya gari amma har zuwa yanzu bai taba amsa gayyatar mu ba, mu kuma doka ce ta kafa mu don haka za ta yi aiki a kan kowa”.
Barista Mahmud ya kuma ce, da zarar hukumar ta kammala tattara bayanai akan Dambazau din za ta bayyana mataki nag aba.
Da yake batu kan koken wasu al’umma a Kano kan batun filaye, gida je da gonaki Barista Mahmud Balarabe ya ce “Za mu bincika koken al’ummar karamar hukumar Kumbotso kan yadda aikin layin dogo ya janyo musu rasa mahallansu ba tare da an biyasu diyya mai kyau ba”
“Mun sani gwamnatin tarayya ce ta ke yin aikin, sai inda aka samu matsalar shi ne rashin tuntubar hukumomin mu da su ma’aikatan kamfanin da yake aiki yayi, wanda kuma mun zauna da su mun fara tattauanwa”.
Shugaban ya kuma ce, a ranar Litinin mai zuwa ne hukumar za ta kafa kwamitin da zai bibiyi matsalar domin magancewa kamar yadda Freedom Radio ta rawaito.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.