Labarai

Gidauniyar Almuhibbah ta horas da Masu bukata ta musamman kan dabarun sana’oi

Daga Zainab Faruq 

Ranar masu bukata ta musamman ta kasa da kasa wata dama ce ta tunasarwa kan nauyin da ke wuyan kowa da kowa kan jan hankali wajen bada dama wa kowa da kowa da kuma daidaito ga kowa da kowa a fadin duniya.

Tana kuma bada dama wajen bayyana jajircewa, nasarori da kuma gudumawar da masu bukata ta musamman ke bayarwa a cikin al’uma.

Wannan wani bangare ne na jawabin da uwargidan gwamnan jihar Bauchi Hajiya Aishatu Bala Abdulkadir Muhammad ta gabatar a wajen bikin ranar masu bukata ta musamman tare da horas dasu kan dabarun sana’oi wanda asusun kula da yawan al’uma na majalisar dinkin duniya UNFPA ya shirya da hadin gwiwar gidauniyar Almuhibbah.

Wakiliyarmu Zainab Faruq ta kasance a ofishin uwargidan gwamnan jihar Bauchi inda aka yaye mutane sama da sittin bayan horas da su kan dabarun sana’oi dabam dabam a wani bangare na bikin ranar masu bukata ta musamman ta kasa da kasa.

Da take jawabi ga wadanda suka ci moriyar tallafin, Hajiya Aishatu Bala Muhammad wacce ta assasa gidauniyar Almuhibbah ta ja hankalinsu da suyi amfani fa kayayyakin sana’oin da aka raba musu ta hanyar da ta dace, don su taimaki kansu sannan su ilmantar da ‘ya’yansu domin ilimi na taka muhimmiyar rawa wajen samar damammaki wa masu bukata ta musamman daidai da kowa.

Ta kuma yi kira garesu da su gujewa barace barace akan titi domin hakan koma baya ne ba zalla ga daidaikun mutane masu bukata ta musamman ba, harma da al’uma baki daya.

Hajiya Aishatu Bala Muhammad tasha alwashin ci gaba da aiki da abokan jera tafiya wajen samar da ayyukan yi da kuma shigowa da masu bukata ta musamman cikin lamuran rayuwa don su ma ana damawa dasu.

A wajen taron ko’odinetan asusun yawan al’uma na majalisar dinkin duniya Deborah Tabara ta karanto sakon shugaban asusun wanda ya bayyana gudumawar da masu bukata ta musamman ke bayarwa a cikin al’uma.

Ta ce kowacce daya cikin mata biyar a fadin duniya na fama da wani nau’i na nakasa, wanda hakan ke jefasu a hatsarin cin zarafi ya kuma hanasu kaiwa inda suke son zuwa, a don haka ne asusun majalisar dinkin duniya ke hada gwiwa da kungiyoyin masu bukata ta musamman, wanda hakan ya taimaka gaya wajen rage girman matsalar.

Da take yabawa gidauniyar Almuhibbah da kuma ofishin uwargidan gwamnan jihar Bauchi bisa ci gaba da hadin gwiwar, ta kuma bayyana alwashin UNFPA na ci gaba da fafutukar kare hakkin BilAdama da kuma damawa da masu bukata ta musamman, musamman mata da yara kanana.

Asusun na kasa da kasa ya kuma tabbatar da aniyarsa na tsayawa a bayan masu bukata ta musamman a fadin duniya, a kiran da suke yi a kare musu hakkokinsu da kuma tallafawa shugabancinsu wajen samar da al’uma mai cike da zaman lafiya.

Wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar tallafin da suka zanta da Albarka Radio sun yi bayani yadda aka horas da su kan dabarun sana’oi dabam dabam tare da yabawa asusun UNFPA da gidauniyar Almuhibbah bisa wannan shiri da acewarsu zai tallafawa rayuwarsu.