Breaking News

Google Zai Raba ₦75m Ga ‘Yan Kasuwa 15 Masu Rabo

Google ya sanar da bude aikace-aikacen asusun Hustle Academy SMB, asusu na kyauta N75 miliyan ga masu kasuwanci . An sadaukar da wannan asusu ne domin inganta muradun kanana da matsakaitan masana’antu na Najeriya (SMEs).

A cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu ta Google ta ce za a raba Naira miliyan 5 ga kananan ‘yan kasuwa 15 na Najeriya a wani bangare na kudurin ta na bunkasa harkokin kasuwanci a Najeriya.

Kamfanin na fasahar ya kara da cewa an tsara wannan tallafin ne kan yadda kananan ‘yan kasuwa ke zama kashin bayan tattalin arzikin Najeriya amma suna fama da kalubale, musamman matsalolin da ke kawo cikas wajen samun kudade masu muhimmanci.

Aikace-aikacen Asusun Hustle Academy suna buɗe daga Yau, Juma’a 28 ga Satumba, 2023 kuma za a rufe ranar Alhamis, Oktoba 12, 2023.

Tushen Labari: LEGIT NG.

Danna Nan Domin Nema.