Labarai

Gwamnan Kano Ya Yi Hayar Lauyan Tinubu Ya Wakilci Shari’arsa A Kotu

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dauki hayar fitaccen lauyan nan, Cif Wole Olanipekun (SAN) domin ya wakilci shari’arsa a Kotun Daukaka Kara.

Aminiya ta ruwaito cewa a watan da ya gabata ne Kotun Sauraron Karar Zabe ta Jihar Kano ta sauke Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar, inda ta ayyana Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.

Da yake kalubalantar hukuncin kotun, Abba Kabir Yusuf ya gabatar da korafi a gaban Kotun Daukaka Kara da hujjoji har guda 42, inda ya bukaci kotun ta yi watsi da hukuncin sannan kuma ta yi watsi da karar da APC ta shigar.

A kunshin karar da Abba Kabir Yusuf ya shigar, Aminiya ta lura cewa, Cif Wole Olanipekun (SAN), wanda ya jagoranci lauyoyin da su ka kare Shugaba Bola Tinubu a shari’ar zaben Shugaban Kasa tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi, shi ne zai wakilci tasa shari’ar.

Haka kuma, a cikin tawagar lauyoyin Gwamna Abba akwai; Bode Olanipekun (SAN) da Ibrahim G. Waru da Akintola Makinde, yayin da Cif E.O.B. Offiong zai ci gaba da kasancewa lauyan na APC.

Jaridar Aminiya