Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Kwace Filin Jirgin Saman Gombe

Gwamnatin Tarayya ta bada izinin kwace ikon gudanar da Filin Jirgin Sama na Jihar Gombe.

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar ne ya sanar da hakan a Fadar Shugaban Kasa, yana mai cewa matakin zai bayu ga samar da karin kayan aiki da kudaden gudanarwa gami da ingantuwar aiki a filin jirgin.

Gwamnan ya bayyana a ranar Juma’a cewa, “Mafi mahimmanci shi ne komawan Filin Jirgin Sama na Gombe hannun Gwamnatin Tarayya da Shugaba Buhari ya amince.“Tuni Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta fara gina barikinta a hafabar filin jirgin , wanda iya ya koma hannun Gwamnatin Tarayya zai samu karin kayan aiki da na gudanarwa, musamman tunda filayen jiragen sama na cikin jerin ayyuka na musamman a karkashin doka. 

“Hakan na nufin za a samu karin kayan aiki da gudanarwa mai inganci kuma za a fada shi ta yadda ayyukan tattalin arziki za su habaka saboda samuwar filin jirgin, wanda zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci.”

A watan Yuni ne Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAAA) ta gudanar da bincike kan kayan aikin Filin Jiragen Sama na Gombe, har ta sahale masa izinin jigilar maniyyata aikin Hajji zuwa kasar Saudiyya.

Game da ziyararsa Fadar Shugaban Kasa, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce ya je ne domin yin godiya bisa muhimman ayyukan ci gaba da Gwamnatin Tarayya ta yi a Jihar Gombe.

Ya ce ayyukan za su bunkasa harkokin tattalin arzikin da samar da ayyukan yi tare da dakile ayyukan ’yan ta’adda da rahotanni suka tabbatar cewa sun fara taruwa a yankin Gandun Dajin Wawa-Zange da ke jihar.

Ya ce manyan ayyukan saun hada da na gyaran babbar titin Gombe zuwa Bauchi, wanda shi ne ya dangana har zuwa Yobe har zuwa Maiduguri.

Sauran ayyukan sun hada da na fadada aikin samar da ruwa na Gombe, wanda ya ce shi ne babbar hanyar samar da ruwa ga garin Gombe da yankunan da ke makwabtaka da shi

Leave a Reply