Latest:
Labarai

Hukumar DSS ta ce Akwai Barazanar Harin Ta’addanci Da Sallah

Hukumar tsaron farin kaya, DSS ta ce ƴan ta’adda na shirin kai hare-hare a masallatan idi da wuraren shaƙatawa lokacin Sallah Babba.

Kakakin DSS, Dr Peter Afunanya ne ya sanar da haka a ranar Alhamis.

Don haka ya buƙaci duk masu kula da wuraren taruwar mutane irinsu kasuwanni da wuraren shaƙatawa da su kai rahoton duk motsin da basu amince da shi ba ga jami’an tsaro.

Ya ce DSS ta ƙwato abubuwa masu fashewa daga hannun waɗanda take zargin ƴan ta’adda ne.

Dr Afunanya ya ce hukumar ta kuma kama makamai da albarusai daga wurin ƴan ta’adda a kan hanyar Abuja – Keffi cikin jihar Nassarawa.

Aminiya

Leave a Reply