Home Labarai Jami’ar IBB Ta Umarci Malamanta Da Su Koma Bakin Aiki

Jami’ar IBB Ta Umarci Malamanta Da Su Koma Bakin Aiki

Jami’ar IBB Ta Umarci Malamanta Su Fice Daga Yajin Aikin ASUU Su Koma Aji

Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU) da ke Lapai a Jihar Neja ta umarci malamanta da su koma bakin aiki ranar Litinin 5 ga watan Satumba mai kamawa.

Hukumargudanarwar Jami’ar IBBU ta kuma umarci lakcororin da su yi watsi da yakin aikin da Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) domin fara darussan zango na biyu na shekarar karatu ta 2021/2022.

“Ana bukatar dalibai da su bi wannan umarni, an dauki wannan mataki saboda su ne,” in ji sanarwar da Mataimakin Rajistara a Fannin Yada Labarai, Alhaji Baba Akote, ya fitar.

Ya bayyana cewa Majalisar Amintattun IBBU ta ba da umarni ga daukacin ma’iaktan jami’ar da su koma bakin aiki ne a zaman majalisar na 55 da ya gudana a ranar Talata.

Amma a martaninsa, Shugaban Kungiyar ASUU Reshen IBBU, Dokta Kudu Dangana, ya ce yajin aikin da suke gudanarwa na nan daram, kuma ba za su bi umarnin komawa bakin aiki ba.

Ya kara da cewa tuni ma suka mika wa shugabancin jami’ar takardar sanarwar tsawaita yajin aikinn wata shida da ASUU ta gudanar zuwa na sai abin da hali ya yi; Don haka ya yi mamakin sanarwar da jami’ar ta fitar.

“Duk dalibin da ya koma makaranta, to kudinsa da lokacinsa kawai zai yi asara, ko kuma kawai sai dai ya tarar babu kowa a jami’ar. Ba mu janye yajin aiki ba,” in ji shi.

Hakazalika, Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aiakatan Jami’a (SSANU), wanda kuma shi ne Shugaban Gamayyar Kwamitin Aiki da Cikawa (JAC), Adamu Isah, ya ce har yanzu suna kan bakarsu ta yajin aikin.

Ya ce Kwamitin Amintattun Jami’an ya kafa kwamitin sasanta wa da kungiyoyin amma hukumar gudanarwar jami’ar ta bi bayan fage wajen ba da umarnin dawowa aiki.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.