Latest:
Labarai

Ko kadan banyi nadama ba kan Rushe-rushen da nayi – Gwamnan Kano

 

Daga Ibrahim Aminu Riminkebe, Kano

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce bai yi nadama ko kadan ba a kan aikin rushewa da kwato dukiyoyin al’umma da gwamnatin da ta shude ta yi ta mallaka ba bisa ka’ida ba tare da raba wa shanu masu tsarki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero tare da hakimai da sauran ‘yan majalisar Masarautar kano, suka kai wa Gwamnatin kano ziyarar barka da sallah a gidan gwamnati a wani bangare na bukukuwan Sallah.

“yace mai Martaba yana da kyau majalisar masarautar ta lura cewa, mun fara aikin rusau ne domin dawo da kadarorin jama’a da aka mallaka ba bisa ka’ida ba, kuma za mu tabbatar da cewa an dawo da duk irin wadannan kadarorin domin maslahar mutanen Kano”.

Alhaji Abba Kabir ya yabawa mai Martaba sarki da ‘yan majalisar masarautun bisa wannan ziyarar wadda ita ce irinta ta farko tun bayan hawansa mulki tare da lissafta nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin kwanaki 31 da suka gabata a bangarorin; biyan kudin NECO Ga daliban makarantun sakandire 55,000 da suka kai naira biliyan 1.5, gyara fitulun tituna da rage matsalar sace-sacen waya a cikin birnin Kano.

Sauran a cewar Gwamnan sun hada da; sake dawo da tantancewar bayar da tallafin karatu na kasashen waje ga ’yan asalin Kano masu digiri na farko, da gaggawar biyan albashi da fansho da kwashe dubunnan tankokin sharar gida a cikin birni.

Tun da farko Sarkin ya ce sun kai ziyarar ne domin taya Gwamnan murnar bikin Sallah tare da ba da tabbacin cewa a shirye yake ya bayar da shawarwarin da za su kasance masu muhimmanci ga ci gaban jihar, ya kuma yi kira ga gwamnati da kuma jama’a da su taimaka wa masu karamin karfi wajen ciyar da jihar gaba. illolin cire tallafin man fetur.

Leave a Reply