Labarai

Kotu ta ɗaure wani matashi shekara 2 bisa satar jannareton masallaci da  kunnashi a gidan Karuwai

Daga Fa’izu Muhammad Magaji

Wata Kutun shari’ar Muslunci mai lamba biyu da ke zama a birnin Bauchi ta ɗaure wani tashi tsawon shekaru biyu a gidan Yari, bayan samun sa da laifin sace wasu kayyakin amfanin wani masallaci a jihar Bauchi da ke Gabashin Najeriya.

Matashin mai suna Lawan Mohammad, ɗan kimanin shekara 25 a duniya wanda yake zama a anguwar Kur da ke Bauchi an gurfanar da shi gaban kotun ne bayan Ƴan Sanda sun kama shi da zargin sace kayyakin masallacin.

Kayan da aka yi zargin ya sata sun haɗar da Jannareto, da ƙimar kuɗin sa ta kai Naira dubu ɗari biyu da kuma man fetur lita goma wanda kuɗin sa ya kai Naira 6200.

Matashin ya kuma saci Fanka ta sama, wadda kuɗin ya kai Naira 15000, kuma ƴar yawo wato Estetion wanda ta kai Naira 5000, sai kuma kofar daya ɓalle wadda kuɗin gyaranta ya kai Naira 20,000.

Mai karanta ƙara ya faɗawa kotun cewa bayan ya sace kayyakin ne, ya tafi wata unguwa da Karuwai ke taruwa wadda ake kira Bayan Gari ya kama ɗaki tare da karuwansa, ya tayar da Jannareton masallacin suka cigaba da shaƙatawa, da Fetir ɗin masallacin.

Bayan an karantawa matashin laifin da ake zargin sa da shi gaban kotun, nan take ya amsa laifin sa, inda Alkalin kotun Barrister Mukhtar Adamu Bello Yamban, ya yanke masa hukumci ɗaurin shekara biyu ba tare da zabin biyan tara ba.

Leave a Reply