Latest:
Labarai

Kotu Ta Haramta Kama Tsohon Gwamnan Kano Ganduje.

Daga Ibrahim Aminu Riminkebe, Kano.

Wata babbar kotun tarayya dake zaman ta a Kano Karkashin Mai Shari’a A. E. Liman ta haramta duk wani yunkuri na kamawa ko gayyata ko tozarta tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ko iyalin sa koma duk wani da yayi aiki Karkashin gwamnatin sa.

Cikin karar da lauyan tsohon gwamna, Barista B. Hemba ya shigar a madadin wanda yake karewa, Kotun ta haramta kwace musu kadarori har sai an saurari karar dake gaban Kotun.

Leave a Reply