Labarai

Kotu Ta Soke Zaben Dan Majalisar NNPP A Kano

 

Kotun sauraron kararrakin zabe a Jihar Kano ta soke nasarar da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Tarauni, Mukhtar Yarima na jam’iyyar NNPP ya samu.

Kotun, wacce ke sauraron kararrakin zaben ’yan majalisun jihohi da na tarayya ta yanke hukuncin ne yayin zamanta na ranar Alhamis.

Kotun dai ta ce ta soke zaben ne saboda zargin badakakar takardun karatun dan majalisar.

Dan takarar jam’iyyar APC, kuma tsohon dan majalisar mazabar, Hafizu Kawu ne ya kai karar yana kalubalantar sahihancin takardun na Yarima.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply