Latest:
Labarai

Kungiyar Lauyoyi Ta Kasa Tasha Alwashin Hukunta Lauyoyi Da Aka Samu Da Hannu A Kwashe Kayayyakin Taron Kungiyar

Kungiyar lauyoyi ta kasa NBA ta tabbatarda faifan Video dake nuna yadda aka kwashe wasu kayayyaki da aka Samar domin rabawa a wajen Taron kungiyar da wasu lauyoyi suka aikata.

Shugaban kungiyar ta NBA Olumide Akpata shine ya tabbatarda faifan Videon, inda yasha alwashi wa al’ummar kasa cewa kungiyar lauyoyin zata dauki mataki akan duk Wani lauya da aka samu da hannu wajen fasa wajenda aka ajiye kayayyakin dama satan wayoyin salula, cin mutunci wasu jami’ai a cibiyar, inda ya tabbatarda za’a hukunta su.

Shugaban kungiyar ta NBA ya bayyana cewa musabbabin faruwar lamarin nada nasaba da tsaiko da aka samu wajen raba kayayyakin da aka ajiye a cibiyar, inda yace hakan kuwa ya faru ne a sakamakon rashin kyawun jakunkunan.

Ya kuma kara da cewa wannan dalilin ne ma ya sanya Kungiyar taki amincewa da kayayyakin.

Akpata yace an dauki wannan mataki ne domin tabbatarda lauyoyin sun samu ingantattun jakunkuna masu inganci a yayin taron.

Leave a Reply