Labarai

Kungiyar Miyetti Allah Da Hadin Gwiwar Jami’anTsaro Sun Cafke ‘Yan Fashi A Jihar Kwara

Wata tawagar hadin kai ta ‘yan sanda daga rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara tare da mambobin kungiyar Miyetti Allah ta Fulani makiyaya ta kama wasu mutum hudu da suka dade suna yi wa ‘ya kasuwa da makiyaya fashin kayansu da dabbobinsu a karamar hukumar Ifelodun ta jihar.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an kama mutanen da ake tuhuma da aikata wadannan laifukan, kamar haka: Bello baneri da Umaru Shehu Auwalu da Mamma Muhammed wadanda dukkansu mazauna rugar Fulani da ke Oro-Ago ne bayan da suka kai wa wani Alhaji Yaya Ishaku hari yayin da yake komawa gida daga kasuwa kuma suka raba shi da naira 600,000.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar ta Kwara Ajayi Okasanmi ya tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin da safiyar ranar Laraba.

Sai dai ya ce an kwato naira 400,000 daga hannun wadand ake tuhuma da yin fashin, cikin naira 600,000 da suka sace wa Alhaji Yahaya Ishaku.

Leave a Reply