Labarai

Kyandar Biri Ta Bulla Kasar Morocco

Morocco da Sudan na gudanar da bincike kan zargin ɓullar kyandar biri. Kamar yadda hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta Afrika CDC ta bayyana, an tabbatar da cewa mutum 1405 sun kamu da cutar haka kuma akwai mutum 62 da suka rasu inda ake zaton cutar ce ta kashe su.

Duka waɗannan an same su ne a ƙasashe huɗu inda aka samu ɓullar cutar.

Hukumar CDC ta buƙaci duk wanda ya ji alamun cutar a tattare da shi ya garzaya asibiti domin gwaji.

Haka kuma an bayar da shawara ga ƙasashen Afrika da su mayar da hankali wajen gudanar da gwajin cutar da kuma sa ido.

Leave a Reply