Labarai

Majalisar Dokokin Jihar Adamawa Ta Samar Kudirin Tilasta Yin Gwajin Miyagun Kwayoyi

Majalisar dokokin jihar Adamawa za ta gabatar wa gwamnan jihar kudirin dokar da ke buƙatar wajibantar yin gwajin kwayoyi, barasa da sauran miyagun kwayoyi ga wadanda ke neman a mukamai, daukar aiki da masu neman guraben shiga makarantu (admission).

Bayan tattaunawa da nazari, a wannan Juma’ar, kakakin majalisar, Aminu Abbas Wanda ya jagoranci zaman majalisar ya bukaci ra’ayin yan majalisar kan batun, wanda duk suka amince shi nan take.

Ya kuma umurci shugaban kwamitin kula ka’idoji da harkokin majalisar da ya sanya ranar da ya dace domin yin karatu na Uku a kan kuɗirin dokar.

Dan majisa, Kabiru Mijinyawa ne dai ya gabatar da kudirin, Wanda Idan aka amince dashi zai zama wajibi ayi gwajin miyagun kwayoyi ga duk Mai neman gurbin karatu a makarantun gwamnatin jihar tare da wani Abu Mai kama da hakan.

Leave a Reply